Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles dake tarayyan Najeriya Paul Onuachu, ya shiga cikin tarihi a fagen wasan kwallon kafa bangaren kasa da kasa.
Paul Onuachu, ya kasance dan wasa na biyu wanda ya zura kwallo a raga cikin mafi karancin lokaci da fara wasa.
Ya samu wannan nasaranne bayan da ya jefa kwallo cikin dakika 7 (Seven Second) a ragar Masar cikin wasan sada zumunci tsakanin kasa da kasa da akayi ranar Talata 26 ga watan Maris 2019, a filin wasa na tunawa da Stephen Keshi dake Asaba Najeriya inda aka tashi 1-0.
Onuachu ya kasance na biyu cikin jerin 'yan wasa da suka jefa kwallo a kankanin lokaci a matakin wasan kasa da kasa a duniya. Bayan dan wasan Jamus Lukas Podolski wanda ya jefa tasa a dakeka 6 kacal (six seconds) a wasan su da Ecuador a shekara 2013.
Facebook Forum