Yankunan mutanen kasar Kamaru masu magana da harshen Ingilishi a kasar sun dai-daice, tun bayan wani farmaki da ‘yan sanda suka kai a yankin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 30 a cikin kwanaki biyu.
Sabon fadan ya kaure ne kusan sati daya da rantsar da shugaba Paul Biya, wanda yayi gargadi ga ‘yan a ware da su ajiye makamansu, ko kuma a kashesu.
A yau Laraba ne mai magana da yawun rundunar sojojin kasar Colone Didier Bedjeck, ya fada cewa an samu karuwar mace-mace, biyo bayan arangama da aka samu na ‘yan kwanaki, inda yace yawan mutanen da aka kashen sun cira zuwa fiyeda 30.
Mai magana da yawun kungiyar ta ‘yan aware Ivo Tapng, kuma ya shaida ma kamfanin dillancin labarai na Reuters, cewar mayakansu biyu ne kawai suka mutu, amma su kuwa sun kashe sojoji gwmnati 13.
Facebook Forum