Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya amince da kafa kwamitin tantance kadarorin jihar mai mambobi 14 domin bincikar gwamnatin mutumin daya gabace shi, Godwin Obaseki.
Sakataren yada labaran gwmnan, Fred Itua, ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi.
A cewarsa kwamitin, da za’a rantsar a gobe Talata 26 ga watan Nuwambar da muke ciki, a fadar gwamnatin jihar dake birnin Benin, zai kasance karkashin jagorancin Dr. Ernest Afolabi Umakhine.
A yayin da Anslem Ojezua zai kasance mataimakin shugaban kwamitin, Frank Edebor zai zamo sakatarensa.
Sauran mambobin kwamitin sun hada Kassim Afegbua da Patrick Ikhariale da Taiwo Akerele da Patrick Idiake da kuma Rasaq Bello-Osagie. Har ila yau akwai karin mambobi irinsu Fredrick Unopah da Abdallah Eugenia da Patrick Obahiagbon da Kenny Okojie da Lindsey Tes-Sorea da kuma Abass Braimoh.
A jawabin daya gabatar yayin karbar rantsuwar kama aiki a ranar 12 ga watan nuwamban da muke ciki Okpebholo ya sha alwashin cewar gwamnatinsa za ta binciki yadda aka mayar da wasu ‘yan majalisar dokokin jihar 14 saniyar ware a 2019.
Dandalin Mu Tattauna