Farfasa Rufai Ahmed Alkali shi ne mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin siyasa. Ofishinsa ne kuma ya kaddamar da kwamitin tantance kungiyoyin dake marawa shugaba Jonathan baya a takarar shekarar 2015.
Farfasa Alkali yayi bayani akan dalilin daukan wannan matakin yayin da ya kai ziyarar gani da ido lokacin da ake tantance kungiyoyin a jihar Kaduna. Banda matsayinsa na mai ba shugaban shawara akan siyasa sai suka lura cewa akwa kungiyoyi da yawa kusan dubu biyar suna kiransa ya fito a sake zabensa a shekarar 2015. Wasu suna son su mara masa baya. Dalili kenan suka sa wani babban kwamiti karkashin Dr Nanka. Sun tafi suna aikin tantance kungiyoyin yau wajen kwana bakwai.
Saidai lokacin da wasu 'yan jam'iyyar PDP suka karkata akan sake tsayawar shugaba Jonathan wasu kuma suna ganin suna da wani dan takara amma ba Jonathan ba. Hajiya Hauwa Garba Kazaure wata marubuciya 'yar jam'iyyar PDP tace gwamna Sule Lamido zasu jaraba a shekarar 2015. A ganinta gwamna Sule Lamido yana matsayin uba ne ga 'yan Najeriya gaba daya.
Dangane da ko gwamnan zai iya kafada da kafada da shugaban dake kan mulki yanzu tace abun da ake nema ga shugaba shi ne yin abun da talakawa suke bukata. Shin yayi abun da zai taimaki al'umma. Tace Sule Lamido yayi minista ya samu nasarar kashi sittin cikin dari a ma'aikatar. Ya zama gwamnan jihar da ya tarar da ita kamar an yi yaki an tashi amma ya aiwatar da ayyuka da kowa. Kowa ya zo jihar yanzu zai yaba. Idan dai batun shugabanci ne Sule Lamido zai iya yin kafada da kafada da duk wani dake neman takara a Najeriya.
Kawo yanzu babu wani dan jam'iyyar PDP da ya fito yana neman yin takara saidai shugaban kasan da Sule Lamido su ne suka nuna alamu.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.