Jamhuriyar Niger na daga cikin nahiyar kasashen Africa da matasan su suka ci gajiyar shirin YALI daga shekarar da aka bullo dashi cikin shekarar 2014 kawo yanzu.
‘Yan kasar ta Niger kimanin 26 ne suka samu horon watanni 6 a jamioin Amurka daban-daban, akan ayyukan ci gaban Al’umma.
Malama Aisha Maki mamba ne a kwamitin dake kula da aikin rajistan YALI, ta bayyana cewa a wannan karon ofishin jakadanci Amurka a Niger na fatan rubanya adadin matasan kasar sau biyu ko sau ukku domin ba Al’umma ta Niger damar cingajiyar ta shugaba Barrack Obama.
‘’Abinda nake son in kwatanta wa duk daukacin matasa na nan Niger na wadanda suke so su tafi cikin tsari na kasar Amurka, shine sharadi na
farko shine shekaru 25-35 ne, duk irin aikin da kake yi kana iya zuwa can kayi kuma kana da damar tafiya, ba batun wai sai wani nada digiri ko kuma difuloma.Abin dubawa shine wane irin aiki ne kake ganin kasar taci gaba?Sharadi na biyu shine ace mutun ace ya iya turanci wato Ingilishi, dan kana da ka iya tunda watanni ukku za ayi kafin a tafi idan an zabi masu tafiya don haka kana iya shigowa cikin kungiyar nan domin ka kara kwarewa a turanci kafin tafiyar ta taso’’.
Ga Sule Mummuni Barma da Karin bayani 2’54