Nura ya ce sana'arsa ita ce sayar da babura a hannu guda, kuma malamin makaranta ne, sannan a wani yunkuri mai dogaro da kai, har ila yau kuma yana waka domin nishadantarwa, da kuma fadakarwa.
Nuran Gwanja ya ce, ya shafe shekaru 9 yana waka, sannan ya fara waka ne tun makarantar Islamiya inda yake wakokin ban kwana wa mata da suka yi aure.
Ya ce babban jigonsa a masana’antar nishadi ba wani ba ne illa Ado Gwanja, sakamakon yana nishadantarwa da fadakarwa ta hanyar nishadi, inda yakan isar da sakon da ya dace.
Ya ce kamar kowanne mawaki, yana fama da rashin fahimta daga bangaren al’umma inda ake yi masa kallon abin da ya ke yi, ma’ana harkar waka, maimakon ya kara tarbiya, da karatu, yana haifar da tabarbarewar al’ada da tarbiya ne a cikin al’umma.
Nuran Gwanja ya ce wakar ita ce hanya mafi sauki da ke isar da sakon shafin sadarwa na zamani, alal misali a wata wakarsa da ya yi, na yadda mata ke kashe mazajensu a yanzu, wakar ta taimaka ainun wajen isar da illar yin hakan.
Ga cikakken rahoton hirar daga wakiliyar DandalinVOA Baraka bashir.
Facebook Forum