Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ba da umurnin a binciki shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan kasar ta NPA, Hadiza Bala Usman, kamar yadda kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya tabbatar.
Wata sanarwa da Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren Alhamis, ta kuma ce shugaban ya umurci shugabar hukumar ta NPA da ta sauka a mukaminta yayin gudanar da binciken.
“Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shawarar da ma’aikatar sufuri karkashin jagoranci Rotimi Amaechi ta bayar, kan a kafa kwamiti don ya binciki shugabannin hukumar ta NPA.” Sanarawar Garba Shehu ta ce.
“Kwamitin binciken zai samu jagorancin Darektan fannin kula da harkokin sufurin ruwa na ma’aikatar sufurin, yayin da mataimakin darekta na bangaren shari’a zai zama sakatare.”
A cewar Garba Shehu, nan gaba za a nada sauran mamabobin kwamitin binciken.
Sai dai sanarwar ba ta ambaci laifukan da ake zargi ko tuhumar Hadiza Bala Usman da su ba.
Sai dai gabanin kafa kwamitin binciken, rahotanni sun ruwaito cewa an dakatar da ita. Fadar shugaban kasar ta ce an nada Mohammed Koko a matsayin mukaddashin hukumar.
A shekarar 2016 Buhari ya nada Hadiza Bala Usman, a matsayin shugabar hukumar ta NPA.