Masu zanga zangar sun isa fadar shugaban gundumar Tanut din inda mukaddashin sa ya karbesu kuma ya saurari koke koken na su. Sun bayyana ma hukumomin cewa ba tare da bata lokaci ba, suna bukatar a samo mafita ko da kuwa ta janyo musu wutar ne ta hanyar matatar kamfanin man SORAZ tun da yana bangaren Tanut ne.
Su ma magabatan sun jinjina ma masu zanga zangar da yadda suka gabatar da kansu cikin lumana ba hargitsi da ba. Jagoran kamfanin wutar lantarki na Tanut ya ce koyaushe suna cikin gyara tare da neman hanyoyin magance matsalar.
Shugaban Kamfanin Maman Shuaibu ya ce suna sanne da wannan matsalar kuma sun damu da rashin wutar lantarkin a gundumar Tanut, kuma suna kokarin ganin cewa sun kawo gyara nan ba da dadewa ba.
Ya ce dole ne a yi hakuri a bari masu gyara su ci gaba da gyara yadda ya kamata tare da jaddada cewa suna kan yin kokarin ganin an kamala gyaran.
Facebook Forum