WASHINGTON DC - Ana kyautata zaton makwabtan Najeriyar za ta bude iyakar a ranar Juma'a, 22 ga watan Maris da muke ciki da misalin karfe sha biyu na safe agogon Najeriya da Nijar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin Kasar Nijar ta fitar inda ta bada umarnin buɗe wasu manyan iyakokinta da Najeriya da aka fi yawan kaiwa da kawowa.
A baya-bayanan ne Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirta ta Yamma, ECOWAS, ta amince da ta dage wasu takunkumai da ta kakabawa kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.
An gabatar da kudirin ne yayin wani taron kungiyar na musamman kan zaman lafiya da siyasa da kuma yanayin tsaro a yankin kasashen ECOWAS a ranar Asabar a Abuja.
Biyo bayan hakan ne Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bada umarnin gaggauta bude kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar ya kuma umarci a janye dukkanin takunkuman da aka kakabawa kasar nan take.
Hakazalika, Shugaba Tinubu ya janye dukkanin dakatarwar da aka yiwa harkokin kasuwanci da hada-hadar kudi tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, ciki harda dakatarwar da aka yiwa kayayyakin more rayuwa da wutar lantarki daga zuwa Nijar.
A baya bayanan ne wasu mazauna yankunan iyakokin kasashen biyu sun ta'allaka matsalar kan rashin bude iyakoki daga bangaren Jamhuriyar Nijar, tare da nuna fatar za a bude don amfanin kasashen biyu.
Cinikayya da sauran huldayya tsakanin al'ummomin Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun shiga wani mummunan yanayi tun lokacin da aka rufe iyakokin kasashen biyu, inda jama'a ke fatar samun sauki da zaran an bude iyakokin.
Dandalin Mu Tattauna