Jami’ai sama da dubu dake karkashin hukumomin birnin Yamai ne ke fama da wannan matsalar rashin albashi wadanda a cewarsu rabonsu da albashi tun watan Yuni na 2016, saboda abinda ma’aikatar magajin gari ta kira rashin kudi a aljihun gwamnati.
Rashin fahimtar da aka samu tsakanin hukumomi da shugabanin ma’aikata a tattaunawarsu ta baya-bayan nan, ta sa shuwagabanin kungiyar kwadagon kiran taro domin sanar da magoya bayansu halin da ake ciki domin sake duba hanyar da za su bullowa al'amarin.
Malam Hassan Jawondo Usman, daya daga cikin shuwagabanin ma’aikatan, ya ce tattaunawar da aka yi, ba ta yi wani armashi ba domin kudin wata daya ne kawai aka amince za a biya su.
A karshen taron daukacin ma’aikatan da suka hada da masu aiki a ofisoshi da masu gadi da masu aiki a wajan ajiya da dai sauransu sun yanke shawarar ci gaba da yin gwagwarmaya har sai haka ta cimma ruwa.