Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Kiristoci Sun Taya Musulmai Murnar Babbar Sallah


NIGER: Sallah a Nijar
NIGER: Sallah a Nijar

Kiristocin Jamhuriyar Nijer, sun taya musulmai murnar babbar salla ta wannan shekara, tare da yin kira ga bangarorin 2 da su cigaba da yin addu'o'i domin samun zaman lafiya a kasar da ma samun damina mai albarka kasancewar ana huskantar farin rashin samun ruwan saman na wannan shekara ta bana.

Yayin da Musulmi a jamhuriyar Nijer ke cigaba da morewa wa kwanakin babbar sallah ta wannan shekara, kiristoci ne a kasar suka yi anfani da wannan damar domin nunawa duniya irin kyakkyawa dangantaka da yanda suke zaune lafiya lumi da 'yan'uwan su Musulmai, yayin da wadansu kasashe makwabtan Nijer din inda bambancin addini, ke rikidewa zuwa fada ko arangama ko ma abkawa jama'a babu gaira babu daliili a wuraren ibadar su.

Pasto Abubakar Musa shugaban gamayar darikokin addinin kirista na Birni N'Konni, yace sun taya musulmi murnar sallah da ma yin kira gare su, su yiwa kasar addu'a.

A nata bangaren, kungiyar CEDIR dake hada kan mabambanta addinai a Nijer, ta hanyar shugaban ta, tayi marhabin da wannan halaya na nuna da ma kara kawo zaman lafiya a kasar tsakanin Musulmi da Kiristoci.

A kowane lokaci, bangarorin kan taya juna murna da zummar shinfida tubali kyakkyawa na zaman lafiya a Jamhuriyar Nijer tsakanin mutanen da ke da bambancin addini.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Malam Shehu Kanam mai sharhi kan al’amura ya mana karin bayanin matsayin dalilan yawaitar fashewar tankokin man fetur a Najeriya
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:23 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Karin haske akan dalilan dake kawo aukuwar haduran tankar mai a Najeriya da musabbabin karuwar wannan lamari a baya-bayan nan
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Karuwar hadarin tankar man fetur da ake samu a Najeriya, inda a shekaran nan da ba ta wuce kwana 40 ba, an samu munanan fashewar akalla hudu
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:05:15 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG