Tsohon shugaban kasar Nijer ya jagoranci wani gangamin magoya bayan gamayyar jam’iyun adawa na ADR . Alhaji Mahamman Usman dake matsayin dan takarar wadanan jam’iyu ya nuna shakku a game da tsare tsaren zabubukan 2020 da 2021 a bisa la’akari da yadda dan takarar jam’iyar PNDS TARAYYA mai mulki Bazoum Mohammed ya ke ci gaba da rike mukaminsa na minstan cikin gida.
NIJAR: Dan takarar gamayyar jam’iyun adawa ya nuna fargaba dangane da tsare tsaren zabubukan dake tafe

5
Hotunan taron gangamin gamqyyar jam'iyun ADR na tsohon shugaban kasar Nijer Mahaman Usman