Jami’ai a Najeriya sunce akalla mutane 80 ne suka mutu, sakamkon harin boma bomai da aka kai a birnin Jos ranar jumma’a data shige,da kuma arangamomi da suka biyo bayan haka.
Wani jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya,Daniel Gambo yace hukumar ta kidaya gawarwaki 80 a Jos,inda hukumomi suka ce mutane 32 ne aka kashe.
Akasarin wadanda harin na jajiberen kirsimeti ya rutsa dasu suna hada hadar karshe na sayen kayan kirsimeti.
Fashs fashen sun janyo arangamomi tsakanin kiristoci dauke da makamai d a wasu kungiyoyin musulmi ranar lahadi a Jos,har aka kona gine gine,aka kashe akalla mutum daya. ‘Yansanda sun kama akalla mutane uku dangane da fitinar ta ranar lahadi.
Hukumomin Najeriya sunce tarzomar ta baya bayan makarkashiyar siyasa ce, da nufin haddasa husuma tsakanin musulmi da kirista gabannin zaben shugaban kasa da za’a yi cikin watan Afrilun bana.