Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun janye yajin aiki da suka fara Laraban nan, da nufin tilastawa gwamnati ta kara albashi mafi karanci ga ma’aikatan kasar.
Kungiyar kwadago ta Labor Congress,da takwararta ta masu sana’o’I TUC, sun janye yajin aikin ne sa’o’I da farawa,bayan shawarwari da suka yi da gwamnati. Shugabannin kungiyoyin sunce gwamnati ta yi alkawarin fara aiki da Karin albashin nan bada jumawa ba, amma sun yi kashedin zasu dauki mataki idan gwamnati ta gaza cika alkawari da ta yi.
Manyan Kungiyoyin kwadagon biyu sun bukaci gwamnati ta kara yawan albashi mafi karanci a kasar daga dala 50.00 da ake biya ahalin yanzu zuwa dala $120.00, ko wani wata.
Yajin aikin da aka fara laraba, ya sa an rufe Bankuna,makarantu,ofisoshin gwamnati a sassan Najeriya da dama. Kamin janyewar an ayyana yajin aiki na gargadin zai ci gaba har zuwa jumma’a.