Hukumomin Jamhuriyar Niger sun cika alkawuran da suka yiwa 'yan gudun hijira da suka arce daga kasashensu dake fama da rigingimu.
Su dai 'yan gudun hijiran sun yi dandazo ne a birnin Agadez lamarin da ya sa hukumoni a Niger kebe wani makeken fili domin karbarsu tare da tanadar masu wasu muhimman bukatu. An kafa masu tantuna da makewayi da ruwa.
Wannan tanadin ya auku ne a karkashin wani tsari tare da hukumar Majalisar Dinkin Duniya, MDD, dake kula da 'yan gudun hijira ko UNHCR.
Malam Yacuba shugaban ofishin karban bakin haure da 'yan gudun hijira na yankin, ya ce kawo yanzu sun sami mutane 341kuma dukansu 'yan kasar Sudan ne. Daga 'yan Sudan, sai na kasashen Guinea da Nigeria.
Hukumomin Niger sun ce 'yan gudun hijiran zasu jira a sansanin ne har sai an kammala tantance su kafin a san makomarsu akan samun makafa a hukumance, kamar yadda yarjejeniyar kasa da kasa ta shata.
Alhaji Umaru Ibrahim Umaru sarkin Agadez ya kira al'ummomin jihar ta Agadez da su nuna jinkai saboda halin da mutanen da suka arce daga kasashen su ke ciki. Yayinda gwamnati ke taimaka musu, sarkin yayi kira ga masu hannu da shuni su dauki dawainiyar mutanen. Ya kira al'ummarsa da su 'yan gudun hijiran su kwantar da hankalinsu amma dukansu su bi doka da oda.
Kawo yanzu akwai 'yan gudun hijira a jihar ta Agadez sama da dubu uku da yawancinsu sun fito ne daga Nigeria, Sudan, da Guinea.
A saurari rahoton Haruna Mamman Bako
Facebook Forum