Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta jera sahu da babbar abokiyar hamayyata Barcelona, wajen sayen dan wasan PSG Neymar.
Real Madrid ta na tattaunawa da kulob din Paris-saint German, kan dan wasanta na gaba dan asalin kasar Brazil, wanda tuni dama ya gayawa kulob din sa PSG zai bar ta.
Sai dai zakarun na kasar Faransa sun ce babu wani tayi da suka karba akan dan wasan.
Neymar ya koma Paris-saint German ne daga Barcelona a shekarar 2017, akan kudi euro miliyan €222.
Paris-saint ba zata dakatar da batun sayen dan wasanba, matukar za'a mayar mata da abun da ta kashe wajen sayen sa kimanin fam miliyan £200m
Mataimakin shugaban Barcelona Jordi Cardoner, ya ce hakan wani yunkuri ne na sake sanya hannu kan dan wasan mai shekaru 27, da haihuwa domin ta sake mallaka a wannan lokacin.
A lokacin da yake buga wasa a Barcelona, Neymar ya lashe lig na kasar Spain har sau biyu da kuma zakarun turai daya sai FIFA Club World Cup, a cikin shekaru hudu da ya shafe a kulob din.
Haka kuma ya lashe wasanni biyu a jere tare da kungiyar PSG na Ligue 1, a Faransa inda ya zurara kwallaye 51 cikin wasanni 56, da ya buga musu.
Real Madrid ta shiga batun sayen 'yan wasa dumu-dumu a watan Janairun nan bayan da Barcelona take saman teburin bana a mako na 19, inda dukkaninsu suke da maki 40.
Facebook Forum