Kaftin din kungiyar Barcelona Lionel Messi, ya ce Neymar yana da burin komawa kungiyar, haka kuma kungiyar na bukatar shi don ya sake maida ita matakin da bata taba kaiwa ba.
Messi ya kara da cewa ya tabbatar da kungiyar su bata da ingancin da ya kamata, su iya tunkarar gasar zakarun Turai na champions Lig ba tare da dan wasan ba.
Barcelona ta yi wani kukan kura na ganin ta dawo da dan wasan, dan kasar Brazil daga kungiyar Paris St Germain, amma hakarta bata cinma ruwa ba, wanda cinikin bai fada ba a gasar Lig 1.
Messi ya kuma kara da cewa dan wasan mai shekaru 28 da haihuwa Neymar, ya kagu ya koma kungiyar, “Ya na cike da farin ciki game da kowar shi kungiyar, yakan nuna hakan koda yau she, da kuma nuna danasaninsa a kan abin da ya faru." Ya yi duk abin da ya kamata don ya dawo kungiyar, wanda shi ne mafi alheri a gare shi.
Facebook Forum