Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nelso Mandela ya cika shekaru 94 a duniya


Tsohon shugaban Afirka Ta Kudu Nelson Mandela daga tsakiya da wanda ya karbeshi Thabo Mbeki daga hagu, tsohon shugaban kasa wanda ya mutu, De Clerk.
Tsohon shugaban Afirka Ta Kudu Nelson Mandela daga tsakiya da wanda ya karbeshi Thabo Mbeki daga hagu, tsohon shugaban kasa wanda ya mutu, De Clerk.

Yara yan makaranta miliyan goma sha biyu suka rera wakar taya Nelson Mandela, gwarzon yaki da mulkin wariya cika shekaru 94 a duniya

Yau Laraba, yara 'yan makaranta a Afrika ta kudu su miliyan goma sha biyu ne suka raira wakar taya Nelson Mandella, tsohon shugaban Afrika ta kudu, gwarzon yaki da mulkin wariya, murnar cika shekaru 94 a duniya.

Mr. Mandela wanda ya yi murabus daga ayyukan gwamnati, ya wuni tare da iyalinsa a gidansa dake kauyen Qunu. a kudu maso yammacin kasar.

A halin da ake ciki kuma, mutane a duk fadin duniya suka yi mintoci 67 Laraban suna gudanar da ayyukan sa kai na tallafawa masu bukatar taimako. Hakan na nufin minti daya a kan kowacce shekarar da ya shafe yana aikin gwamnati.

Mr. Mandela ya zama shugaban Afrika ta Kudu, bakar fata na farko a alif dari tara da casa’in da hudu, bayan ya shafe shekaru 27 a gidan yari, a saboda gwamnati wancan lokacin ta same shi da laifin yaki da gwamnatin tsirarru ta nuna wariyar launin fata.

XS
SM
MD
LG