Wasu daga cikin shugabannin APC sun rubuta wata takardar koken cewa suna zargin shugaban APC na jihar Neja Engr Muhammad Imam, da yin sama da fadi da wasu makudan kudaden jam’iyar har Naira Miliyan 500, zargin da ya musanta.
Wannan al’amari dai ya sa shugaban amsa wasu tambayoyi daga jami’an tsaro na dan wani lokaci kafin daga bisani aka sallame shi.
Idris Umma Liman Gban Gba shi ne sakataren kudi na APC kuma daya daga cikin masu wannan zargi ya ce “daukar matakin ya zama tilas saboda shugaban ya danne komai kuma ba ya barin a gudanar da aiki na jam’iyyar.”
Shugaban sashen walwalar jama'a na APC a jihar ta Neja Alh. Muka Rijau ya ce kudaden da suke zargin shugaban ya yi kwana da su sun kai Naira Milyan 500 saboda haka ya ce maganar ba karama ba ce.
Shi dai shugaban na APC na jihar Neja Engr Muhammad ya yi watsi da wannan zargi inda ya ce ba shi da tushe balle makama domin wadanda suka rubuta zargin ba su da shedun da za su tabbatar da gaskiyar zargin.
Duk da yake har yanzu gwamnatin jihar ba ta ce komi ba akan lamarin, amma tuni masu sharhi ke alakanta wannan dambarwa da rashin cikakkiyar jituwar da ke akwai tsakanin bangaren gwamnatin jihar Nejan da kuma shugaban APC.
Saurari rahoton a sauti.
Facebook Forum