Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nan da yan kwanaki za'a gabatar da jadawalin gwamnatin wucin gadin Libya

Shugaban Majalisar mulkin wucin gadi ta Libya, Mustafa Abdel Jalil.
Shugaban Majalisar mulkin wucin gadi ta Libya, Mustafa Abdel Jalil.

Majalisar mulkin wucin gadi ta kasar Libya tace nan da yan kwanaki zata bada jadawalin kafa gwamnatin rikon kwarya ta kasar. Mai magana da yawun Majalisar da ake cewa NTC a takaice, Abdel Hafiz Ghoga ya bada sanarwar cewa gwamnatin rikon kwarya zata kunshi ministoci ashirin da biyu da kuma mukadashin Prime Minista.

A halin da ake ciki kuma, a jiya juma’a mayakan majalisar NTC, suka kaddamar da hari akan birnin Sirte, garinsu tsohon shugaba Moammar Gaddafi. Sun kaiwa birnin hari da manyan bindigogin igwa a kokarin da suka sake yi na fatattakar magoya bayan Gaddafi.

Haka kuma sojojin na yan tawaye suna kuma fafatawa a Bani Walid. Mayakan na yan tawaye suna fuskantar turjewa sosai a wadannan birane guda biyu daga magoya bayan Gaddafi.

Haka kuma a jiya juma’a wata yar Gaddafi mai suna Aisha, ta gabatar da sakon da aka dauka akan faifai, tana mai fadin cewa babanta Gaddafi yana na daram kuma yana fafatawa kafada da kafada da magoya bayansa.

Wani gidan talibijin na Syria ne ya gabatar da sakon, wanda a ciki Aisha ta kuma zargi sabbin shugabanin Libya akan cewa maciya amanar kasa ne, tana mai fadin cewa wasun su da ai suna cikin gwamnatin Gaddafi ne.

A watan jiya Aisha da maihafiyarta da yan uwanta maza guda biyu sun arce zuwa Algeria bayan da mayakan Majalisar NTC suka kutsa birnin Tripoli. Har yanzu dai ba’a san inda Moammar Gaddafi yake ba.

XS
SM
MD
LG