Sabanin abun dake faruwa a wasu kasashen duniya, musamman kasashen da suka ci gaba, a Najeriya nakasassu sun ce suna cikin wani yanayi na rashin samun kulawar da ta kamata daga mahukuntan kasar.
Sai dai akwai bayanan tanade tanade da aka ce wasu gwamnonin kasar sun yiwa nakasassun domin inganta rayuwarsu amma har yanzu basu daina korafin rashin gani a kasa ba.
A jihar Kano wakilin Muryar Amurka dake birnin Kanon, Mahmud Kwari ya ce an yiwa nakasassun "ta leko ta koma ne" a ranar Lahadin da ta gabata. Ya ce ba'a taba kawo kayan tallafi ba a ranar tunawa da nakasassun domin a inganta rayuwarsu. Abun mamaki, inji Mahmud Kwari shi ne a inda aka ce su hallara ranar domin a tallafa masu nan suka yini amma babu alamun jami'an gwamnati ko wata hukuma, saboda haka a karshe sai suka watse. Wannan injishi ya jawo korafe korafe.
A bangaren gwamnati sun alakanta rashin kasancewarsu da nakasassun ne akan shirye-shiryen da suke yi na tarban shugaban kasa, Muhammad Buhari, dalili ke nan da suka dage batun ba nakasassun tallafin da suka shirya bayarwa jiyan. A cewarsu zasu sa sabuwar ranar da za'a rabawa nakasassun kayan tallafin.
A jihar Sokoto wakilin Muryar Amurka Murtala Faruk Sanyinna ya ce duk da yake a can baya akwai wasu kudaden alawus da ake ba nakasassun har yanzu suna korafi. Suna ganin akwai wasu abubuwan da ya kamata a yi masu.
Hassan Umar Tambuwal wakilin Muryar Amurka dake kudu maso yammacin Najeriya, ya ruwaito daga Ibadan babban birnin jihar Oyo yana cewa gwamnatocin jihohin suna kula da nakasassun amma 'yan asalin jihohinsu.
Shugaban guragu a jihar Neja, Malam Awal Ahmad ya bayyana halin da suke ciki a jihar. Ya ce ba'a sa shugabannin nakasassu a harkokin gwamnati ba sai dai a sa wasu a ce su ne suke kula da harkokin nakasassun.
A jihar Kaduna ce kadai lamarin ya banbanta saboda wakilin Muryar Amurka Isa Lawal Ikara cewa ya yi har da mukami gwamnan jihar ya ba nakasasshe. Gwamnan ya nada wani makaho a matsayin mai bashi shawara akan harkokin nakasassu.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Facebook Forum