Shugabannin kungiyar sun nuna damuwarsu a lokacin da suke ganawa da manema labaru a cibiyar 'yan jarida ta jihar Kaduna.
Munktari Sale sakataren yada labarai na kungiyar makafin arewacin Najeriya yace sun ji gwamnan jihar da majalisar dokokin jihar sun makawa dokar hana bara hannu ba tare da tuntubarsu ba ko tare da yawunsu ba, kuma basu san inda dokar ta nufa ba. Yace saidai an gaya masu ba zasu je su yi bara ba ba tare da yi masu wani tanadi ba.
Muntari yace an yi irin dokar a Kano da Legas amma bata yi anfani ba. A Abuja ma an yi bata yi tasiri ba. Ginin ma da aka yiwa nakasassu Abuja ya zama banza. Yayi zargin cewa gwamnatin da suka zaba ita ce kuma ta juya zata ci masu mutunci.
A bangaren mata nakasassun sun mika kukansu ga Allah da manzonsa. Yadda suka yiwa PDP warwas haka zasu yiwa APC a Kaduna.
Su ma 'ya'yan nakasassun sun bayyana nasu ra'ayin. Sun ce sun taimaka gwamnan ya ci zabe yanzu kuma zai wulakanta masu iyaye. Suna cewa kamata ya yi a ba iyayensu abun da zasu yi kafin a hanasu bara.
Amma mai taimakawa gwamnan jihar ta fannin nakasassu Alhaji Aliyu Maikyau wanda shi ma makaho ne da yake aiki da gwamnan yace gwamnati tana da tsarin da zata taimakawa rayuwar nakasassu. Yace kafin a tsayar da dokar an nemi ra'ayin duk masu ruwa da tsaki. Yace bukatarsu ita ce a samar masu abun yi. Wani babban bukatarsu kafin su amince da dokar shi ne a yi masu hukuma da zata kula da harkokinsu.Yace bukatar tana gaban majalisa kuma za'a kaiga kafa hukumar.
Kafin a kafa hukumar gwamnati zata inganta wuraren da suke koyon sana'o'i tare da inganta makarantunsu da kuma kara shigowa da kayan aiki da zasu taimaka masu.
Ga karin bayani.