A koyaushe hukumomin Nijar na kiran nakasassu su daina bara su koyi sana'a su daina mayar da bara sana'a.
Duk da kiran na gwamnati nakasassun sun ce har yanzu basu gani a kasa ba. Suna sarafa kayayyaki da dama saboda da horaswar da suka samu amma ba'a sayen kayansu.
Nakasassun na kera abubuwa da dama amma gwamnati bata taba basu kwangilar kera wani abu ba ko a matsayin tallafi.
Nakasassun na kera abubuwa da dama. Suna dinki. Suna saka kujeru ta makafi. Suna aikin katako da na fata. Suna makanikanci. Babban burin nakasassun shi ne su ga 'yanuwansu nakasassu sun bar bara sun shiga sana'a.
Sun kira gwamnati ta rika basu aiki domin su dogara da kansu.
Madam Sani Aishatu direkta a ma'aikatar gwamnati, tace ta kan hadasu da NGOS domin samun taimako. Haka kuma gwamnati ta dauki nakasassu aiki kamar makafi zuwa aiki a wasu wurar.
Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.
Facebook Forum