Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Sake Ciwo Bashin Naira Biliyan 850


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Majalisar Dokokin Najeriya ta baiwa Shugaba Muhammadu Buhari izinin ciwo bashin wasu kudade har Naira Biliyan 850, kamar yadda ya nema a wata wasika da ya aike wa majalisar.

Shugaba Buhari ya ce, cutar coronavirus ce dalilin daukan wanan mataki amma a wannan karon bashin zai dauki wani salo ne na daban.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan ne ya karanta wasikar bayan majalisar ta kwashi kusan sa'o'i biyu tana zaman sirri.

Wasikar tana kunshe ne da dalilan da ya sa kasar ta rage Kasafin kudin wanan shekara domin faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce, shigowar cutar coronavirus kasar ce ke neman gurgunta tattalin arzikin kasar kuma a wanan yanayi, dole ne Majalisar Dokoki ta hada hannu da bangaren Gwamnati wajen ceto kasar daga mumunan durkushewa, ganin cewa an kwashe makwanni 6 kenan da ba a yin aikin komi a kasar, sabili da bullar cutar COVID-19, kuma wannan bashi za a ciwo mafi yawan sa ne a cikin gida Najeriya ba daga kasar waje ba.

Sanata mai wakiltan Kaduna ta Tsakiya Uba Sani, ya kara jadadda muhimmancin daukan matakan taimakawa kasar, ganin cewa al'umma suna bukatan dauki ta fannoni da dama kama daga fanin kiwon lafiya da abinda lafiya za ta ci.

kwararre a fanin tattalin arziki Shuaibu Idris Mikati ya ce, annoba ce da ta shigo duniya baki daya ta sa kasar a cikin wani hali na ha'ula'i wanda dole ne a ciwo bashi, kuma Najeriya na daya daga cikin kasashen da karfin arzikin ta ya kai a ba ta wannan bashi.

Kasafin kudin da Buhari ya tura Majalisar ya ragu daga Naira Triliyan 10.594 zuwa Triliyan 10.276 kazalika an rage kiyasin farsahin danyan mai a kasuwar duniya daga dalar Amurka 57 zuwa 30 kuma an rage adadin gangar man da za a rika hakowa a rana daga miliyan 2.7 zuwa 1.7, bugu da kari an kara farashin dalar Amurka daga Naira 305 wanda aka gina kasafin kudin akai zuwa Naira 360.

Majalisar Dokokin ta sake tafiya hutun sai baba ta gani a bisa dalilin takunkunmin hana yawo da mahukuntar kasar suka gindaya saboda dakile yaduwar cutar coronavirus.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG