A wata sanarwa da cibiyar dake yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta fitar, ta ce an samu karin mutum 9 da suka kamu da cutar coronavirus a jihar Osun, biyu a jihar Edo, sai kuma daya a jihar Ekiti. Yanzu jimlar wadanda suka kamu da cutar ta kai 151 a Najeriya.
Tuni dai aka sallami mutane 9 daga asibiti, sannan kuma mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon cutar.
Sanarwar ta kuma ce jihar Legas ita ce a kan gaba da mutane 82, daga nan sai birnin Abuja mai mutane 24, mutane 14 a jihar Osun, sai kuma 8 a jihar Oyo.
A ganawar da ya yi da manema labarai, Ministan Lafiyar Najeriya Dakta Osagie Ehanire, ya ce yanzu haka an samar da cibiyoyin kwantar da marasa lafiya da zasu dauki mutune 1000 a birnin Abuja, tare da kayan aiki na zamani kuma tuni aka umarci sauran jihohi suma su samar da irin wadannan asibitocin na wucin gadi domin tunkarar wannan cuta.
Yanzu haka dai ana ci gaba da aiki da dokokin hana yawo da Shugaban
kasa Muhammadu Buhari ya sanar a farkon makon nan. A wata hira da Muryar Amurka, Dakta Bashir Yankuzo na jami’ar kimiya da fasaha dake Minna, ya ce matakin ya yi daidai kuma akwai bukatar 'yan kasa su bi doka domin kare kansu da sauran al’umma daga kamuwa da wannan cuta.
A saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum