‘Yan wasan kwallon kwando sahun mata ‘yan Najeriya wato D’Tigress, za su kara da shahararrun takwarorinsu na Amurka, a kokarin neman gurbin shiga gasar wasanni ta Olympics da za a yi a birnin a badi.
Baya ga Amurkan, 'yan wasan na D'Tigress za kuma su fafata da Serbia da Mozambique a wasannin neman shiga gasar wacce Japan za ta karbi bakunci.
A jiya aka sanar da jerin kungiyoyin da za su gwabza da ‘yan Najeriya a wani takaitaccen biki da aka gudanar a kasar Switzerland, wanda ya bayyana fara karawar ta neman gurbin.
A cewar shugaban hukumar kwallon raga, Injiniya Musa Kida, ya ce shiga cikin gasar Olympics ta 2020 ba karamin jan aiki ba ne, amma abu ne mai yiwuwa.
Karanbatta da kungiyar za ta yi ta farko a duniya da Amurka da wasu kasashen 7, ba zai zama karamin aiki ba, amma a shirye suke, kuma za su shiga cikin gasar.
Tawagar maza sun tsallake, yanzu haka ido na kan tawagar matan don su ma su tsallake don shiga jerin sahun wadanda za su kara a gasar ta Olympics.
Facebook Forum