Asiwaju Bola Tinubu, wanda bai cika yin magana a kan halin da kasar ta ke ciki ba tunda jam’iyarsa ta karbi mulki sama da shekaru biyar da suka shige, ya bayyana cewa, kasar tana cikin rikici kama daga matsalar mahara, da ‘yan bindiga dadi, da kuma abinda ya shafi matsalolin tsaro baki daya.
Shugaban jam’iyar mai mulki ya bayyana haka ne yayin addu’ar Firda’u na gwamnan farin kaya na farko a jihar Lagos Lateef Jakande, da aka gudanar a gidanshi dake Ilepeju.
Bola Tinubu ya bayyana cewa, duk da yake kasar tana fuskantar tashe tashen hankali da kalubalen tsaro, Allah ya albacin kasar ta fannoni da dama, zai kuma taimaka wajen ganin ci gabanta.
Shugaban Jam’iyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya su karamta marigayin ta wajen maida kalubale da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu a dinke Baraka da ricikin kabilanci da na addini da kasar ke ciki. Ya ce ‘yan Najeriya basu da wata kasa ko kuma wuri da zasu je da ya wuce kasar su.
yan-najeriya-sun-bukaci-a-zauna-lafiya
an-saka-dokar-hana-fita-a-jihar-oyo-saboda-rikicin-kabilanci
kura-ta-lafa-a-wani-rikici-da-ya-barke-a-wata-kasuwar-legas
Bisa ga cewar shi, duk wanda ya ga yaki da kuma illar yaki ba zai taba so Najeriya ta shiga wannan yanayin ba. Sabili da haka ya yi kira ga al’ummar kasar su kai zuciya nesa su rungumi zaman lafiya da kyakkyawan zamantakewa da juna.
Karin bayani akan: Asiwaju Bola Tinubu, Nigeria, da Najeriya.