A Nigeria, har yanzu ana ci gaba da farautan mutumen nan da akace shine jagoran harin da aka kaiwa kiristoci ranar Kirsemeti, wanda kuma ya arce yayinda yake hannun ‘yansanda, wanda har gwamnati tace zata bada goron Naira milyan hamsin ko dala dubu 300 ga duk wanda ya taiamaka mata kama shi.
Jami’ai sunce a ranar Laraba ne wannan mutumen da ake kira Kabiru Sokoto ya gudu lokacinda wasu ‘yan bindiga suka shiga artabu da ‘yansandan da yake a hannunsu, zasu kai shi ma’ajiya.
Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan dai ya lasa takobin zai kori shugaban ‘yansandan Nigeria Hafiz Ringim daga aikinsa idan har ya kasa faraito Kabiru Sokoto kafin yau Jumu’a. Shi kansa kwamishinan ‘yansandan da ke jagorancin ‘yansandan da suka kamo shi Kabiru din, Zakari Biu, yanzu haka an dakatar da shi daga nasa aikin.
Wannan al’amarin ya kara janyowa ‘yansandan Nigeia zargin cewa su dai kam ba zasu iyatsaron lafiyar al’umma ba, to amma kakakin ‘yansanda Olusola Amore yace suna iya bakin kokarinsu don su sake cafko Kabiru Sokoto.