Najeriya ta kara yawan lambobin girma da ta samu a wajen wasanni zagaye 12 na Afrika da aka yi a kasar Morocco, inda ta kara yawan lambobin da yawan zinare da azurfa da kuma tagulla a wasannin raga na Badminton da kwallon Kwando da daukar kayan nauyi.
kamfanin dillanci labarai na Najeriya shine ya bada rahoton cewa: Tawagar 'yan wasan Najeriya ta lashe lambobin zinare shida a gasar daga nauyi da kuma azurfa uku a Gasar Cin Kofin Afirka a Morocco. An gudanar da taron mai kayatarwa a filin wasa na Nahda da ke Salle Nahda.
Tsohon dan wasan dambe na kasa, Emmanuel Appah, ya lashe lambobin zinare uku a gasar daga nauyi ta maza, mai nauyin kilo 61, bayan da ya dauke jimlar nauyin kilo 271, tare da nauyin kilo 120.
Adijat Olarinoye ita kuma ta lashe zinare biyu da azurfa daya, a gasar daga dauyi ta mata, mai nauyin kilo 55, ya yin da tsohowar gwarzuwa ta kasa, Chika Amalaho, itama ta lashe lambobin zinare daya da kuma azurfa 2 a gasar.
A halin yanzu Najeriya na da lambobin girma, zinare 12, azurfa 11 da tagulla 12 a gasar Afrika da aka yi a kasar Morocco.
Facebook Forum