Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kwaso Sama Da Mutum 6000 Da Suka Makale a Kasashen Waje 


Wani jirgin kasar Pakistan
Wani jirgin kasar Pakistan

Tun bayan bullar cutar Coronavirus, an mayar da jimullar 'yan Najeriya 6,317 gida wadanda suka makale a kasashen waje sakamakon rufe filayen jiragen sama da aka yi a sassan duniya.

Shugabar hukumar da ke sanya ido kan 'yan Najeriya mazauna kasashen waje NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da ta yi da manema labarai.

Ta ce an kwaso mutum 806 daga Amurka, mutum 831 daga Birtaniya. Sai kuma mutum 117 daga kasar Saudiyya, 372 daga Habasha, 70 daga Faransa da kuma 540 daga kasar Indiya.

Kana a cewar Erewa, akwai mutum 1,045 da aka mayara da su gida daga Hadadiyar Daular Larabawa, sai mutum 324 daga Turkiyya da kuma mutum 365 daga kasar Sudan.

Wani jirgin kasar Birtaniya
Wani jirgin kasar Birtaniya

Ta kara da cewa an mayar da mutum 172 Najeriyar daga kasar Uganda da Kenya, sai 324 daga Afirka ta kudu sai kuma 205 daga Ghana da dai sauransu.

Har yanzu ba a bude zirga-zirga jiragen kasa-da-kasa ba a kasar, sai dai ministan harkokin sufurin jiragen sama Hadi Sirika, ya ce yana sa ran za a iya farawa kafin watan Oktoba mai zuwa.

Ya fadi hakan ne cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kuma ya kara da cewa "ba a gama yanke hukuncin lokacin da za a fara sufurin jiragen kasa-da-kasa ba."

Tun a cikin watan Maris dai aka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa-da-kasa a Najeriyar sakamakon kokarin da ake yi na takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG