Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kuduri Aniyar Kammala Aikin Shata Iyaka Da Kamaru


AGF ABUBAKAR MALAMI AND MAHAMATANNADIF
AGF ABUBAKAR MALAMI AND MAHAMATANNADIF

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta dukufa sosai wajen tabbatar da an kammala aikin shata iyakar ta da kasar Kamaru.

Ministan shari’a na Tarayyar Najeriya Abubakar Malami ne ya bayyana hakan a yayin da Wakilin Sakatare Janar na mussaman na Majalisar Dinkin Duniya na yankin Yammacin Afirka da Sahel Mahamat .S. Annadif ya kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja.

Malami ya ba da tabbacin cewa za’a aiwatar da sauran ayyukan da suka rage don shawo kan matsalolin rashin jituwa kan iyakokin Kamaru da Najeriya gaba daya kuma za’a ayyana su bisa tsari na doka nan gaba.

A cewar Malami "abin alfahari ne idan har aka yi nasarar shawo kan duk wata matsala da ake fama da ita a kowane yanki da ke iyaka da Najeriya da Kamaru, kuma a ayyana shi ba tare da nuna tsoro ko son zuciya ba amma bisa tsarin hukunci na doka ta Kotun kasa-da-kasa’’.

AGF ABUBAKAR MALAMI AND MAHAMATANNADIF
AGF ABUBAKAR MALAMI AND MAHAMATANNADIF

Ana sa ran shirin tattaunawa da Hukumar Hadin Kan kasar Kamaru da Najeriya (CNMC), wanda za’a gudanar a Yaounde babban birnin kasar kamaru zai taimaka wajen share fagen samun nasarori masu tarin yawa ciki har da aikin shata iyakokin kasashen biyu.

Mahamt Annadif ya yi jinjina kan fahimtar juna da kyakyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu tare da cewa wannan mataki ya yi nuni da cewar Yan’Afirka da kan su za su iya magance matsalolin yankin Afirka a Afirka.

XS
SM
MD
LG