Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa, ta kara damara domin ganin ta magance yadawa kananan yara cutar kanjamau. Daya daga cikin matakan da gwamnatin ke shirin dauka shine, aiwatar da shirin Hukumar lafiya ta Duniya da ake kira “Option B Plus”.
Darekta janar na cibiyar yaki da cutar kanjamau na kasa farfesa John Idoko ne ya bayyana haka a wajen taron yaki da cutar kanjamau na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Washington DC.
Gwamnati zata dauki kwararan matakan cimma muradin karni da kuma rage yada kwayar cutar kanjamau daga uwa zuwa jariri da kimanin kashi casa’in bisa dari kafin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, da kuma tallafawa mata masu juna biyu dake dauke da kwayar cutar kanjamau.
Farfesa Idoko ya bayyana cewa karancin kudi yana gurguntar da yunkurin cimma wannan burin, dalilin da kuma yasa daga cikin dakunan kula da mata masu juna biyu dubu takwas da dari uku da sittin da ake da su, dari shida da sittin kadai suke kulawa da matan dake dauke da kwayar cutar kanjamau.
Ya kuma bayyana takaicin ganin yadda kimanin kashi 50% na mata masu juna biyu a yankunan karkara basu zuwa awo duk da kokarin da gwamnati ke yi na samar da gidajen awo a yankunan karkara.