Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na kan hanyar Wargajewa, Tana Bukatar Daukin Gaggawa - Gwamnonin PDP


Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi.
Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi.

Gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyar PDP sun bayyana cewa Najeriya na bukace da samun kyakkyawan shugabanci, domin magance barazanar wargajewa da take fuskanta.

Wata sanarwar bayan taron gwamnonin na PDP da suka gudanar a Makurdi, babban birnin jihar Benue, ta bayyana bukatar gaggauta sake fasali da garambawul ga tsarin kasar, wadda suka ce ta tabarbare a karkashin mulkin gwamnatin APC.

Gwamnonin na PDP sun koka akan yadda “kasar ke ta samun koma baya sakamakon rashin tsaro, da tabarbarewa dangantaka tsakanin rukunonin al’umma daban-daban.”

Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi
Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi

Sun zargi gwamnatin ta APC da kirkira gibi da bambance-bambance tsakanin ‘yan kasa, wanda a cewar su, “ya haifar da tashe-tashen hankula da ke da alaka da kabilanci, rikice-rikicen addini da na siyasa, da sauran nau’o’i daban-daban na ayukan assha.”

Jagororin na adawa sun ce “Najeriya ba ta cancanci sake komawa a cikin wani yakin basasa ba,” don haka suka yi kiran da a gaggauta sake fasalin karfin ikon gwamnati a dukkan matakai, “domin ya zama wajibi a halin yanzu.”

Gwamnonin na PDP sun koka akan cewa hannuwansu a daure suke ta yadda ba su iya ceto al’ummominsu daga mawuyacin halin da suke ciki ba, a yayin da gwamnatin ta APC ta yi kaka-gida da mulkin kasar, kuma take yin yadda ta ga dama.

Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi
Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi

Akan haka suka ce “lokaci yayi da za’a yi amfani da fafutukar garambawul da ake yi wa kundin tsarin mulki, domin rage karfin ikon gwamnatin tarayya musamman a sha’anin samar da tsaro, a kuma kara saka gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi.”

Haka kuma sun yi kira ga hukumar nan ta raba arzikin kasa, da ta gaggauta aikewa da sabon tsarin raba arzikin kasa da zai kara kudade ga jihohi da kananan hukumomi, zuwa ga shugaban kasa da majalisar dokoki domin daukar mataki.

Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi
Gwamnonin PDP Sun Yi Taro A Makurdi

Gwamnonin da suka halarci taron na Makurdi a karkashin jagorancin shugabansu kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, sun hada da Nyesom Wike na Rivers, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Godwin Obaseki na jihar Edo, Bello Matawalle na Zamfara da Ifeanyi Okowa na jihar Delta.

Sauran sune Seyi Makinde na jihar Oyo, Ahmadu Fintiri na Adamawa, Duoye Diri na Bayelsa, Udom Emmanuel na Akwa Ibom, Darius Ishaku na Taraba, da mai masukinsu gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, kazalika da wasu mataimakan gwamnonin na PDP da ke wakiltar gwamnoninsu.

To sai dai duk wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ita ko jam'iyyar APC mai mulki ta gudanar da nata taron shugabanni a Abuja, inda ta nuna amincewa da goyon bayan ta kan yadda shugaba Muhammadu Buhari yake tafiyar da shugabancin kasar.

XS
SM
MD
LG