A karon farko, an sami bullar cutar coronavirus a karamar hukumar Daura dake jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya, wato karamar hukumar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Wani likita ya rasa ransa sanadiyar cutar a farkon makon nan.
Kawo yanzu, bayanai daga cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya sun nuna cewa adadin wadanda suka kamu da wannan cutar a Najeriya ya kai 254, yayin da aka sallami masu jinya 44, wasu su 6 kuma suka riga mu gidan gaskiya.
A halin yanzu mutane 130 ne ke dauke cutar a jihar Legas, 50 a birnin tarayya Abuja, 20 a jihar Osun, sai kuma jihohin Oyo da Edo inda kowannensu ke da mutum 11.
Sannu a hankali dai wannan cuta ta tunkaro jihohin arewacin Najeriya, inda jihar Bauchi ke da mutum 6 yanzu, ciki har da gwamnan jihar. Daga na sai jihar Kaduna mai mutane 5, a nan ma ciki har da gwamnan jihar, sai mutum 1 a jihar Benue, Kwara 2, daga nan sai kuma jihar Katsina da a baya bayan nan cutar ta hallaka wani likita a garin Daura.
A halin da ake ciki kuma, shugabannin Majalisar Dattawa da ta wakilan Najeriya sun yi Allah wadai da matakin rarraba tallafin gwamnatin tarayya, suma al’ummar kasar sun yi kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan cewa suna da bukatar kayan tallafin yayin da suke kulle a gidajensu.
Gwamnatin jihar Niger, a ta bakin kwamishinan lafiyarta Mohammed Makun Sidi, ta ce yanzu haka an killace wasu mutane su 27, bayan da aka gano cewa sun yi mu’amalla da wani da ya dawo daga jihar Legas kuma ya nuna alamun kamuwa da wannan cuta ta COVID-19.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Babangida Jibrin.
Facebook Forum