Yanzu haka dai 'yan Najeriya sun maida hankali kan cika alkawalin kamfen ga wadanda su ka lashe zabe, a tarayya da jihohi. Baya ga batun kararrakin kalubalantar zabe a kotu.
Ga shugaba Buhari da ya samu tazarce karo na biyu na alwashin cika alkawarin mataki na gaba da hakan ya hada da buda gwamnatin sa don ba wa bangarori damar ba da gudunmawa.
Babbar jam’iyyar adawa da ta kai 'kara don kalubalantar sakamakon, ta ce ta na sa ran amshe madafun iko daga hukuncin kotu, don APC na alkawari ba a gani a kasa.
Dr. Abubakar Kari na cibiyar Dimokradiyya ya bayyana irin kalubalen da ke fuskantar gwamnatin Buhari, da hakan ya hada har da rashin cimma nasara ta zahiri a yaki da cin hanci.
Har yanzu dai manyan jam’iyyu biyu ne keda tasiri a Najeriya da hakan ke nuna indai manufofin su na da tasiri, za a samu sauyi inda hakan ba lalle ya zama abun dubawa ba don sauya shekar ‘yan siyasa daga nan zuwa can.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum