Wannan sanarwa ta fito ne a ranar Larabar data gabata 15 ga Yunin shekarar nan da mu ke ciki. To amma wasu masu fashin baki suna ganin cewa, idan aka yi abinda ya dace akan iya cimma gaci.
To amma in aka bi sabanin haka to tabbas za a sami tangarda a lamarin. Masanin kasuwanci kuma Daraktan cibiyar kasuwanci, masana’antu, ma’adanai da ayyukan noma na jihar Kano Alhaji Attahiru Magaji Gwarzo, ya tattauna da wakilinmu.
Inda ya bayyana matsalar yadda aka bawa ‘yan kasuwa wannan lasisin, to ta ina dalar zata shigo? Ya fadi cewa, in dai a haka za’a tafi ba linzami balle dorewar tsari, to Nairar Najeriya zata ci gaba da rugurgujewa.
Domin kuwa kudin za su ci gaba da karanci, sannan bukatarsu za ta fi yawan dalar da take zagayawa a gari. Wani dan kasuwa Alhaji Najib Muhammad Tukur mai sana’ar hada-hadar kudaden kasashen ketare.
Yace wannan ba zai haifar da da mai ido ba, domin dan kasuwa riba yake nema, don haka idan ya samo canji da tsada haka zai tsadantar da ita ga masu saye.
Talakawama sun koka da cewa jifan a kansu zai fado, domin sune hannu baka hannu kwarya. ga sautin rahoton daga bakin wakilinmu na Kano Mahmud Ibrahim Kwari.