Naja Yakasai- Daga cikin kalubalen da ta ke fuskanta shi ne, yadda mutane suke yanke hukunci dangane da abubuwa da ba su da tabbas a kai ba, mussaman ma ga su mata, inda al'umma ke yawan yanke musu hukuncin da bai dace ba.
Naja Yakasai, matashiyar mawakiyar nanaye, wakokin soyayya da ma wakokin biki baya ga na fadakarwa da ta ke yi a wasu lokuttan.
Ta ce ta fara waka ne sakamakon yabon manzon Allah, da suka faro tun lokacin tana makarantar Islamiyya, daga bisani sai kwatsam ta tsinci kanta tana wakokin fadakarwa, da ma na siyasa domin wa’azantarwa da kuma samu kudaden shiga a lokaci guda.
Duk da waka abinda take shawa’a ne, duk wanda ya ce yana sana’a toh lallai duk yadda hajjar da zata kawo kudi yake sayarwa, don haka ne ma take yawan fitar da wakoki na gada ko na biki.
Waka ta yi mata komai na rufin asirin rayuwa na jin dadi, da kuma kashe bukatan da suke gabanta.
Facebook Forum