Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

“Na Fi Messi, Pele Da Maradona Iya Kwallon Kafa", Inji Cristiano Ronaldo


Kafin wannan lokaci, ana kwatanta Ronaldo da Messi ne da Pele-wanda ya lashe kofin duniya sau 3-da Maradona da ya lashe gasar a 1986.

Tauraron kwallon kafa dan asalin Portugal Cristiano Ronaldo ya ayyana kan sa da dan wasan daya fi kowa iya taka leda, inda ya fifita kan sa akan babban abokin hamayyarsa Lionel Messi da diego Maradona na Argentina da kuma gwarzo Pele na Brazil.

An jima ana muhawara akan dan wasan daya fi kowa fice a tarihin wasan kwallon kafa, inda galibi aka fi takaita gasar tsakanin Ronaldo da Messi. a tsakaninsu su 2 sun lashe kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d’or sau 13-inda dan Portugal ya lashe sau 5 yayin da dodan kwallon kafa dan Argentina ya lashe sau 8.

Kafin wannan lokaci, ana kwatanta Ronaldo da Messi ne da Pele-wanda ya lashe kofin duniya sau 3-da Maradona da ya lashe gasar a 1986.

Sai dai a hirarsa ta baya-bayan nan da La Sexta, Ronaldo yace shi dan wasa ne daya zarta dukkanin mutanen 3 wadanda a lokuta daban-daban ake musu kallon da suka fi kowa iya wasan.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG