Mutum-mutumi na farko mai iya fahimtar muryar mutane na shirin tafiya duniyar wata, can nesa da duniyar bil’adama wanda aka kaddamar a jihar Florida. Wannan shi ne mutum-mutumi na baya-bayan nan da aka inganta shi don taimaka ma ‘yan sama jannati a wajen yin wasu ayyuka a falakin sararin sama.
Mutum-mutumin mai suna CIMON 2, mai yawo ba tare da shamaki ba, na dauke da amsa kuwar makiraho, da kyamara, kana da wata manhaja mai sanar da na’urar akwai wani abu a kusa da ita ko kuma wani na magana da ita.
Cimon 2, bai da nauyi a hannu amma idan aka kwatanta nauyinsa da mutum-mutumin SpaceX Falcon 9 za a ga cewar Falcon 9 na da kimanin nauyin buhun siminti 52. Wanda a dalilin rashin nauyinsa yasa aka dakatar da harba shi a ranar Laraba saboda iska mai karfi da aka samu a ranar.
“Abu mafi muhimmanci a nan shi ne, don a samar wa ‘yan sama jannati abokin hira, saboda kadaici da sukan samu kansu a ciki a lokacin da suke sararin samaniya.” A cewar mai jagorantar wannan aikin kuma wanda ya kirkiri CIMON2, Matthias Biniok.
Biyo bayan sakamakon abubuwan da aka fahimta bayan kamfanin IBM ya kirkiri CIMON 1, shi ya sa aka ga cewar akwai bukatar kirkirar wanda shi kuma aikin shi ne kawai ya dinga nishadantar da mutane a lokacin da basa tare da iyalansu ko dangi.
Facebook Forum