Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 9,007 Suka Warke Daga COVID-19 a Najeriya


Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta fitar sun nuna cewa karin daruruwan mutane sun kamu da cutar COVID-19 a kasar.

A cewar hukumar, mutum 490 ne cutar ta harba wanda hakan ya mayar da gaba dayan adadin zuwa 24,567.

Daga jihohi 20 na kasar aka samu sabbin alkaluman, kuma har yanzu jihar Lagos ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar wadda coronavirus ke janyowa, inda yanzu ta sake samun mutum 118. Sai jihar Delta da ke bin ta da mutum 84.

Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Ebonyi inda aka samu mutum 68, 56 a birnin tarayya Abuja, 39 a Plateau, 29 a Edo, 21 a Katsina, 13 a Imo, 12 a Ondo, 11 a Adamawa, 8 a Osun, 8 a Ogun, 6 a Rivers, 5 a Kano, 3 a Enugu, 3 a Bauchi, 3 a Akwa Ibom, 1 a Kogi, 1 a Oyo, 1 a Bayelsa.

A sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter a daren ranar Lahadi 28 ga watan Yuni, ta kuma bayyana cewa mutum 9,007 suka warke daga cutar yayin da mutum 565 suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG