Akalla mutum 5 aka kashe wasu fiye da 8 kuma suka jikkata a lokacin da wani bom ya tashi a wata cibiyar binciken jami’an tsaro a Baidoa, babban birnin jihar Southwest da ke Somalia, a ranar Asabar 4 ga watan Yuli, a cewar jami’an tsaro da wadanda suka shaida lamarin.
Jami’ai a Baidoa, mai tazarar kilomita kusan 250 yamma da birnin Mogadishu, sun fada wa sashen Somalia na Muryar Amurka cewa ga dukan alama nakiya aka binne a wata cibiyar karbar haraji ta gwamnati a kudancin garin.
“Farar hula 4 da wani jami’in sojan gwamnati ne suka mutu a harin mutum 8 kuma suka jikkata, a cewar kwamishinan gundumar Hassan Mo’alim Bikole. Ya kara da cewa ana jinyar mutanen a asibiti kuma galibin wadanda suka jikkata farar hula ne.
A Mogadishu babban birnin kasar kuma, wani dan kunar bakin wake da ya tuka wata mota ya tsarwatsa kansa a gaban shelkwatar harajin gwamnatin kasar, inda ya jikkata mutum 7 ciki har da jami’an tsaro.
Facebook Forum