Ana zargin 'yan Boko Haram da jefa bom a wata mashayar giya a arewa maso yammacin Najeriya a jiya Lahadi, al'amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 25 da kuma raunata wasu 12 a kalla.
'Yan sanda da shaidu sun ce a kan babura maharan su ka je har mashayar wadda ke wani budadden dandali a garin Maiduguri, sannan su ka wurga bom din cikin taron jama'ar da ke zaune ana shaye-shaye. Wasu shaidun sun ce kuma maharan sun yi harbi da bindigogi cikin taron jama'ar.
Hukumomi na zargin kungiyar Boko Haram da kai harin.
Maiduguri ne babban birnin jahar Borno wadda ta rungumi tsantsar Shari'ar Islama. Ana jin cewa Boko Haram ke da alhakin fasa dimbin boma-bomai, da yin harbe-harbe da kuma kai hare-haren kan 'yan sandan jahar ta Borno.