A daren ranar Laraba 27 ga watan Mayu cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutum 389 da suka kamu da cutar COVID-19.
Hukumar ta NCDC ta ce an samu sabbin kamu mutum 256 a jihar Legas wadda ita ce kan gaban a adadin masu kamuwa da cutar.
Sauran jihohin da aka samu karin sun hada da Katsina inda aka samu mutum ashirin da uku, 22 a Edo, 14 a Rivers, 13 a Kano, 11 a Adamawa, 11 a Akwa Ibom, 7 a Kaduna, 6 a Kwara, 6 a Nasarawa, 2 a Gombe, 2 a Filato, 2 a Abia, 2 a Delta, 2 a Benue, 2 a Neja, 2 a Kogi, 2 a Oyo, 1 a Imo, 1 a Borno,, 1 a Ogun, 1 a Anambra.
Ya zuwa yanzu dai gaba dayan adadin wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 a Najeriya ya kai 8733.
Sanarwar ta kuma ce an sallami mutum 2,501 daga asibiti, bayan haka mutum 254 suka mutu sakamakon cutar.
Facebook Forum