Mazauna yankin Timbuktu dake arewacin kasar mali sun fara tayar da kayar baya ma ‘yan kishin Islama dake kokarin shimfida tsarin shari’a a yankin.
Shaidu a garin Goundam sun ce an fara tayar da kayar bayar ne a lokacin da ‘yan kishin addini na kungiyar Ansar Dine suka daki wata matar da ba ta rufe kanta ba a jiya jumma’a. Suka ce jaririn da matar take dauke da shi ya ji rauni a lokacin da aka far mata.
Shaidu sun fadawa VOA cewa ‘yan zanga-zanga sun kewaye wani masallacin garin suka hana ‘yan kishin addini shiga ciki don sallar Jumma’a.
Suka ce masu kishin addinin sun yi ta harbi a sama domin tarwatsa mutanen da suka taru. Wani mazaunin garin ya fadawa VOA cewa yanzu dai kura ta lafa, koda yake akwai zaman dar-dar.
Garin Goundam yana cikin yankin da ‘yan awaren Abzinawa da masu kishin Islama suka kwace a karshen watan Maris, kuma a yanzu garin baki dayansa yana hannun masu kishin addini, ciki har da na kungiyar Ansar Dine.
Ansar dine ta ce tana son kafa tsarin shari’ar islama a fadin kasar Mali. A cikin ‘yan makonnin nan, kungiyar ta yi ta rusawa tare da lalata hubbaren wasu shaihunan malamai na Sufi a Timbuktu tana mai cewa barinsu sabo ne.