Wani harin kunar bakin waken da aka kai a harabar hedkwatar ‘yan sandan Nijeriya da ke Abuja, ya hallaka akalla mutane biyu, ciki har da maharin. Wannan tashin bam din ana kyautata zaton shi ne kunar bakin wake na farko a Nijeriya.
Wani wanda yayi ikirarin cewa yana magana ne da yawun tsattsaurar kungiyar nan ta Boko Haram, ya ce su suka kai harin a wata hira da Muryar Amurka. Ana zargin kungiyar da kai jerin munanan hare-hare a arewacin Nijeriya da a kan auna kan jami’an ‘yan sanda,da na gwamnati da sauran masu mulki.
‘Yan sanda sun ce an tsaida motar da ake kyautata zaton ita ke dauke da maharin na jiya Alhamis a mashigar hedikwatar ‘yan sandan, aka umurce shi ya karkata zuwa inda aka faka motoci don a bincike shi inda ya tayar da bam din. Sun ce wani mai aikin bayar da hannun da ya shiga motar don ya mar jagora, shi ma ya mutu a tashin bam din.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce akalla mutane 7 sun raunana a tashin bam din; kuma ‘yan sanda sun ce bam din ya lalata motoci 30.
Wakilin Muryar Amurka a Abuja, Nasiru Adamu el-Hikaya, yace babu wani abinda al'ummar Najeriya ke magana kai tun jiya, im ban da wannan lamarin da ya fara tayar da hankulan 'yan Najeriya.
Saurari Rahoton Nasiru Adamu el-Hikaya daga Abuja |