WASHINGTON, DC —
Jarabawar da Hukumar Shige da Fici ta Najeriya ta shirya domin cike guraben aiki kasa da dubu biyar manema aikin fiye da rabin miliyan ne suka kasance wurin.
Turmitsitsin da ya faru ya yi sanadiyar mutuwar mutane ashirin a wasu jihohi na kasar da suka hada da babban birnin Abuja inda mutane bakwai suka mutu.
Misali a babban birnin Fatakwal mutane dubu ashirin da biyar ne suka cika makil a filin dake daukar mutane dubu goma sha shida. A jihar Imo mutane hudu suka sume nan take. A jihar Oyo ma mutane takwas suka sume. Amma a jihar Neja bayan wadanda suka sume an samu rasuwar mutane uku.A Kano ma an samu mutane da suka rasu. Haka labarin yake ko a babban birnin tarayyar Najeriya. Wannan adadin ne ya kai har mutane ashirin.
Cikin wadanda suka rasu har da mata masu juna biyu kana mutanen da ba'a bayyana adadinsu ba suna kwance asibiti sakamakon wannan turmutsitsin.
To saidai kawo yanzu gwamnati bata ce komi ba game da lamarin duk da za'a fara taron makomar Najeriya.
Sai dai tuni jama'ar kasa suka fara tofa albarkacin bakinsu. Tsohon ministan 'yansanda kuma jigo a jam'iyyar APC Yakubu Lame yace sun tabbatar ba'a taba yin gwamnatin da bata iya aiki ba kuma wadda bata damu da halin da 'yan kasar ke ciki ba kamar ta yanzu. Shugabannin yanzu sai abun da ya damesu suka sani. Yace shirya jarabawar a baina jama'a ba kan gaskiya ba ne. Sun yi ne su rudi duniya amma ba domin aiwatar da gaskiya ba. Kafin ma a zo jarabawar an dauki wadanda ake so ko.
Shi kuma sarkin kasuwar Alaba Alhaji Umaru Nagogo cewa ya yi muddin ba shugabannin ba ne saka sake lale ba to haka kasar zata cigaba da zamacikin matsala. Yace duk wani dan siyasa da yake anfani da 'ya'yan talakawa domin cimma muradun kansa aikin banza ya keyi.
Ga rahoto.