Wanda ya fara zantawa da Muryar Amurka a kan taron bude bakin yace ya yi mamaki an gayyaceshi zuwa wurin bude baki duk da cewa shi kirista ne, amma yace ya ji dadi kuma idan aka cigaba da yin hakan za'a samu zaman lafiya domin Allah daya ne.
Kungiyar nan ta wanzar da zaman lafiya tsakanin addinan biyu itace ta shirya taron zaman bude baki da dimbin mabiya addinan biyu a birnin Sokoto tare da hadin gwuiwar ma'akatar kula da lamuran matasa ta jihar Sokoto.
An shirya taron ne domin nuna kauna da karfafa zaman lafiya dake wanzuwa tsakanin al'ummar musulmai da mabiya addinin kirista a jihar Sokoto.
Alhaji Sani Umar Jabbi shi ne ya shugabanci zaman na bude baki. Yace fiye da shekaru dari Allah ya hada musulmai da kirista suna zaune tare kuma basu taba samun wata fitina ba. Yace ganin yadda abubuwa ke faruwa a duniya yau inda wadanda basu san addini ba suna tada hankulan mutane da sunan addini ya sa suka ga ya zama wajibi su shirya irin taron.Yace zarafi ne na nunawa kirista cewa addinin musulunci addini ne na zaman lafiya. Haka ma addinin kirista addini na fadakar da zaman lafiya.
Alhaji Jabbi yace abun da ya fi mahimmanci shi ne su jawo matasa su sani cewa zaman lafiya shi ne ya fi a'ala muddin ba'a hana kowa yin addinisa ba.
Shi ma Rebaran Ahmadu Mamman wanda ya jagoranci kirista a wurin bude bakin yace sun amsa gayyatar da aka yi masu ne domin yin zumunci tare. Yace sun dade suna tare amma wannan wata dama ce ta nunawa matasa cewa ya kamata mabiya addinan biyu su karfafa zaman lafiya. Yace yana farin cikin cewa an zama daya domin kishin kasa da zaman yadda za'a tafi tare.
Ga karin bayani.