Mujallar LIFE & TIMES Ta Karrama Shugaban Sashen Hausa Na Muryar Amurka Aliyu Mustapha Sokoto
Fitacciyar mujallar LIFE & TIMES, wacce ke kan gaba cikin mujallu dake mayar da hankali labaran ‘yan Afirka mazauna Amurka da sauran kasashen duniya, ta karrama shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha Sokoto da lambar yabo ta gogewa a aikin jarida da kuma yiwa jama’a hidima.