Dan wasan kwallon kafa na Liverfool Mohammed Salah ya shirya tsaf don cin kwallon sa ta 50 a kan kungiyar kwallon kafa ta Watford.
Dan wasan dan asalin kasar Egypt, cin kwallo daya ya rage masa ya zama dan wasan mafi sauri a rabin karni acikin kulob guda daya.
A yau laraba Mohamed Salah yana fatan ya zura kwallon sa ta 50 a wasan kwallon kafa ta Premier League a kungiyar sa ta Liverpool a kan kungiyar kwallon kafa ta Watford.
Bayan da ya zira kwallo a wasanni biyar da suka gabata, Mohammed Salah dan shekarun 26, yana fatan ya cigaba da taka leda da tawagarsa tare da burin cin kwallo a kan kungiyar Hornets, wanda da ya zira musu kwallaye shida a cikin wasanni uku da suka gabata.
Bayan zuwansa Roma a shekara ta 2017, Salah ya ji dadin zama farko da kungiyar Reds, inda ya zira kwallaye 32 a kakar wasa ta farko - wannan nasarar da ta rushe tarihi a wasanni 38 da suka buga, a halin yanzu kuma yana jagoranci 'yan wasan da maki 17.
Facebook Forum