Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miyetti Allah Ta Fara Wayar Da Kan Matasa Kan Illar Shaye-shaye Da Bangar Siyasa


Miyetti Allah
Miyetti Allah

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatti Allah a Najeriya ta fara wayar da kan matasan Fulani a kan illar shaye-shayen kayan maye da bangar siyasa.

Kungiyar Miyatti Allah ta kaddamar da wani shiri na musamman da zai mayar da hankali kan wayarwa matasan Fulani kai, kan illar shan miyagun kwayoyi da kuma shiga bangar siyasa.

Da yake kaddamar da shirin a Minna, shugaban kungiyar Miyatti Allah, Alhaji Muhammadu Kiruwa Hardon Zuru, ya ce ya zama tilas su dauki wannan mataki, musamman a dai dai wannan lokaci na shiga hada-hadar siyasa a Najeriya.

Gwamnatin jihar Neja ta yaba da wannan mataki na fadakar da matasan Fulanin da kungiyar ta Miyetti Allah ta dauka. Babban darakta mai kula da harkokin makiyaya a ofishin gwamna, Alhaji Abdullahi Babaye, ya yabawa shugaban kungiyar Miyetti Allah da ya fara gudanar da wannan shirin a jihar Neja.

Yanzu haka kuma kungiyar Fulanin ta fara fadakar da makiyayan muhimmancin tsarin kiwo irin na zamani da zai kawo karshen al’adar zuwa kiwo kasa da kasa, da fulanin ke yi a halin yanzu.

Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG